Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su hada gwiwa wajen kawar da barazanar tsaro
2019-10-30 11:01:36        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bukaci kasashen Afrika dasu hada karfi tare da nufin kawar da barazanar tsaro a Afrikan wanda ya jefa zaman lafiyar nahiyar cikin hadari.

Kwamishina AU mai kula da zaman lafiya da tsaro Smail Chergui, shi ne yayi kiran gaggawar a lokacin wani taron majalisar kwararru na AU, wanda aka gudanar a matsayin wani bangare na babban taron karawa juna sani game da tabbatar da zaman lafiya da tsaron Afrika, wanda aka gudanar ranar Juma'a a kasar Djibouti.

Chergui, ya lura cewa, nahiyar Afrika tana samun gagarumin cigaba wajen yin rigakafin barkewar tashe tashen hankula ta hanyar daukar matakan gaggawa wajen gano barazanar tsaro tare da gaggauta tura jami'an diplomasiyya don kaucewa yiwuwar barkewar tashe tashen hankulan. Ya kara da cewa, daukar irin wadannan matakai suna kara samar da yanayin zaman lafiya da kyakkyawar makoma ga Afrika. (Ahamd Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China