Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya bayyana dalilin da ya sa ministan wajen Sin ya fara ziyarar aiki a Afirka a farkon shekara cikin shekaru 30
2020-01-13 10:27:39        cri
Jiya Lahadi, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da ministan harkokin waje da cinikin kasa da kasa na kasar Zimbabwe Sibusiso Moyo sun gana da 'yan jaridu tare, inda Wang Yi ya yi bayani kan dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan fara ziyarar kasashen Afirka a farkon ko wace shakara cikin shekaru 30 da suka gabata.

Wang Yi ya ce, tabbas ministan harkokin wajen kasar Sin zai fara ziyarar aiki a farkon ko wace shekara daga nahiyar Afirka, sabo da dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, ana iya cewa, Sin da Afirka sun zama 'yan uwan juna. Dadadden Zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka da bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru da dama da suka gabata ya kasance abin koyi ga sauran kasashen duniya, da kuma abin koyi na hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Dalili na biyu shi ne, sabo da bukatun kasashen Sin da Afirka na zurfafa hadin gwiwa da neman ci gaba tare. Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kana nahiyar Afirka nahiyar ce mai kunshe da kasashe maso tasowa mafi yawa a duniya, akwai damammaki da dama wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Na uku kuma, babban aikin dake gaban Sin da Afirka ta fuskar karfafa hadin gwiwarsu a harkokin kasa da kasa da kuma kiyaye moriyarsu ta bai daya. A halin yanzu, akwai matukar bukatar karfafa mu'amalar dake tsakanin Sin da Afirka, domin kiyaye ikon al'ummomin kasashensu wajen nuna adawa da tsoma baki da kasashen ketare suka yi cikin harkokin gidansu, neman daidaito da adalci, da kuma kyautata zaman rayuwarsu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China