Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban kasar Burundi na biyu ya gana da Wang Yi
2020-01-12 16:15:40        cri

Mataimakin shugaban kasar Burundi na biyu Joseph Butore, ya gana da Wang Yi, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, a Bujumbura jiya Asabar.

Joseph Butore ya jinjinawa alakar kasarsa da kasar Sin, inda ya ce, koda yake akwai nisan gaske tsakanin kasashen biyu, amma suna da dadaddiyar 'yanuwantaka. A 'yan shekarun nan, dangantakar kasashen biyu na tafiya yadda ya kamata, har ma an samu dimbin nasarori a hadin-gwiwarsu ta fannoni daban-daban. Gwamnatin Burundi ba zata sauya manufarta ta kulla zumunta da kasar Sin ba koda an samu canzawar halin da ake ciki a kasar.

A nasa bangaren, Wang Yi ya jaddada cewa, Burundi, amintacciyar abokiya ta kwarai ce ga kasar Sin. Kuma Sin ta dade tana bayyana cewa, duk wata kasa, ko babba ko karama, dukka daya ne. Wang ya kuma yabawa gwamnatin kasar Burundi saboda tsayawarta kan manufar kulla zumunci da kasar Sin, inda a cewarsa, ya kamata su marawa juna baya da baiwa juna taimako. Kasar Sin tana nuna goyon-baya ga Burundi don kare cikakken 'yancin kanta, da kiyaye halastaccen hakkinta, a kokarin lalibo hanyar neman bunkasuwa da ta dace da halin da ake ciki a kasar.

Wang Yi, ya sake nanata cewa, ko da duniya na fuskantar wasu manyan sauye-sauye, kasar Sin zata kasance abokiyar arziki da kulla 'yanuwantaka da Burundi har abada.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China