Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi kira da a zurfafa alakar Sin da kasashen Larabawa bisa manyan tsare-tsare
2020-01-08 19:15:26        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira da a zurfafa alakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa bisa manya tsare-tsare, a kuma yi amfani da matakai na siyasa wajen warware batutuwan shiyya masu sarkakiya.

Wang ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin ganawarsa da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa (AL) Ahmed Aboul Gheit a birnin Alkahiran Masar.

Wang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin sahihiyar abokiyar kungiyar kasashen Larabawa ce kuma abin dogaro. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China