Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da takwaran aikinsa na kasar Burundi
2020-01-12 17:01:26        cri
Jiya Asabar, memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya gana da takwaran aikinsa na kasar Burundi Ezechiel Nibigira a Bujumbura.

Wang ya ce, ya kamata kasashen biyu su kara samun fahimtar juna da zurfafa hadin-gwiwa tsakaninsu. Sin tana fatan gudanar da hadin-gwiwar cin moriyar juna tare da Burundi a karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" da wasu muhimman matakai takwas da aka sanar a taron kolin Beijing na dandalin FOCAC, musamman a fannonin da suka shafi muhimman ababen more rayuwar al'umma da ayyukan gona. Kasar Sin zata karfafawa managartan kamfanoninta gwiwar don su zuba jari a Burundi, ta yadda za'a cigaba da taimakawa kasar wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma.

A nasa bangaren, Ezechiel Nibigira yana maraba da zuwan Wang Yi kasarsa, wadda ta zama ziyarar farko da ya yi a sabuwar shekarar da muke ciki, al'amarin da ya nuna cewa kasar Sin na maida hankali sosai kan dangantakar kasashen biyu. Burundi ta godewa kasar Sin saboda taimakon da ta ba ta, kana ta yaba da rawar da Sin ta taka a batutuwan kasa da kasa da na nahiyar Afirka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China