Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tallafawa yakin da duniya take yi da ta'addanci a jihar Xinjiang
2020-01-09 11:01:58        cri

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasar sa ta tallafa matuka, a yakin da duniya take yi da kungiyoyin ta'addanci, ta hanyar sauya tunanin wadanda suke da alaka da irin wadannan kungiyoyi a jihar Xinjiang.

Wang Yi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudana, tare da takwaran sa na Masar Sameh Shoukry a birnin Alkahira.

Ministan ya ce batun jihar Xinjiang harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma dukkanin matakan da ake dauka ba su wuce na yaki da 'yan aware, da 'yan ta'adda ba, sabanin zargi da wasu ke yi cewa, batun na da nasaba da 'yancin bil Adama ko addini.

Ya ce a tsawon lokaci, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, daya ce daga yankuna 5 masu kunshe da kananan kabilun kasar Sin, ta kuma sha fama da matsaloli masu nasaba da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. Kaza lika masu fatan aikata muggan ayyukan ta'adda sun kaddamar da hare hare da dama, wadanda suka sabbaba kisa da jikkatar dubban fararen hula, da ba su ji ba ba su gani ba.

Bisa burin kare rayukan dukkanin kabilun yankin na Xinjiang ne kuma, cikin hadda mabiya addinin musulunci, gwamnatin Sin ke kara azamar murkushe dukkanin nau'o'in ayyukan ta'addanci, a daya hannun kuma ta kafa cibiyar koyar da sana'o'i da samar da horo, domin sauya akalar wadanda suka taba cudanya da irin wadannan kungiyoyi zuwa hanyar da ta dace.

Ya ce matakan yaki da ta'addanci a Xinjiang da gwamnati ke aiwatarwa, sun haifar da kyakkyawan sakamako. Duba da cewa yanzu haka shekaru 3 ke nan a jere, ba a samu wani harin ta'addanci ba a Xinjiang.

Wang ya ce akwai cikakkiyar damar yin addini, ciki hadda musulunci a Xinjiang, jihar da a yanzu haka ke da masallatai da yawan su ya kai sama da 24,000, adadin da ya kai masallaci daya ga duk mutane 530. Ya ce wannan adadi ya dara wanda ake da shi a wasu kasashen ma na musulmi da dama.

Daga nan sai ya soki lamirin mummunar manufar wasu kasashen yamma, a yunkurinsu na gurgunta yanayin zaman lafiya a Xinjiang, da yin zagon kasa ga ingantacciyar alaka dake tsakanin Sin da kasashen musulmi, ta hanyar yada farfaganda, duka dai da nufin dakile ci gaban kasar Sin.

Ministan ya ce kasashen musulmi ciki hadda Masar, ba su rudu da irin wadancan karairayi da wasu kasashen yamma ke yadawa ba. Maimakon haka ma kasashe 51, ciki hadda na musulmi 28, sun rattaba hannu kan wasikar da aka aike zuwa ga MDD a watan Yuli, wadda ke kunshe da goyon bayan matakan da Sin ke dauka a jihar Xinjiang.

Sama da tawagogin kasashen waje 70 daga kasashe da yankuna 91, ko mutane 1,000 ne suka ziyarci jihar Xinjiang, suka kuma bayyana matakan yaki da ta'addanci da ake dauka a jihar, a matsayin matakan da ka iya zama abun koyi ga sauran sassan duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China