Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani jirgin saman fasinja na Ukraine ya fadi a Iran
2020-01-08 13:34:43        cri

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na Iran suka bayar a yau, wani jirgin saman kamfanin jiragen saman Ukraine mai dauke da mutane 180 ya fadi, a dab da filin jiragen sama na Imam Khomeini dake birnin Tehran na kasar Iran a wannan rana, kamar yadda gidan telebijin na kasar Iran ya bayyana, babu wanda ya tsira daga hadarin.

Kamfanin dillancin labaru na Fars na kasar Iran ya bayyana cewa, jirgin saman samfurin Boeing 737 ya tashi daga filin jiragen sama na Imam Khomeini kafin ya fuskanci matsalar na'ura, kana ya fadi a dab da filin jiragen saman. An ce jimillar yawan fasinjoji da ma'aikatan jirgin ya kai 180.

Har yanzu ba a tantance sunaye da asalin fasinjojin dake jirgin saman ba.

Kamfanin jiragen saman kasar Ukraine bai bayar da sanarwa game da batun ba tukuna. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China