Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 32 sun mutu a turmutsitsin jana'izar Soleimani
2020-01-07 20:08:09        cri
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, a kalla mutane 32 ne, suka mutu a wani turmutsitsi yayin da ake jana'izar marigayi Qassem Soleimani yau Talata a birnin Kerman na kasar Iran.

Shugaban cibiyar daukin gaggawa ta kasar Iran Pir Hossein Kolivand ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ISNA cewa, wasu mutane 190 kuma sun jikkata.

A ranar Jumm'a ne dai, wani hari ta sama da Amurka ta kai a filin jiragen sama na Bagadaza na kasar Iraki ya hallaka Qassem Soleimani, tsohon kwamandan dakarun juyin juya halin Islama na Iran (IRGC). (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China