Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta karyata zargin da ake mata da hannu a harin da aka kai sojojin Amurka a Iraki
2019-12-31 10:23:01        cri
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Iran Ali Rabiee, ya sanar a jiya Litinin cewa, babu hannun kasarsa a mummunan harin baya-bayan nan da aka kai wa dakarun Amurka dake kasar Iraki.

Kafar yada labarai ta Press TV, ta ruwaito jami'in na cewa, ikirarin Amurka, ba zai taba zama hujja na yin luguden wuta da kashe mutane ta hanyar keta dokokin kasa da kasa ba.

Rabiee ya ce, harin da aka kai wa sojojin Amurka, ya kara tabbatar da illar rawar da take takawa a yankin, musamman a kasar Iraki, ya kuma sake nuna cewa, muddin Amurka ta ci gaba da zama a kasashen Iraki da Syria, hakika ba za a samu zaman lafiya ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China