Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar riko da akidun jamiyya na gaskiya
2020-01-09 11:17:25        cri

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi kira ga 'yan JKS da su kara azama, wajen riko da akidun jam'iyya na hakika, da rike hakan a zukatansu, ta yadda jam'iyyar za ta ci gaba da kasancewa kan manufarta ta cika alkawari.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar ta Sin, ya yi wannan kira ne yayin wani taron gangami da aka yiwa lakabi da "Tsaiwa kan gaskiyar tushen akida." Ya kuma bayyana cewa idan har ana burin samun amincewar al'umma, to ya zama dole jam'iyya ta rungumi akidunta na ainihi.

An dai fara wannan gangami ne na 'yan jam'iyyar daga matakin sama zuwa kasa a zango biyu, tun daga watan Mayun shekarar da ta gabata, wanda tuni aka kammala kaso mai yawa na ayyukansa, wanda ya kunshi yayata hadin kai, da managarcin tsarin siyasa, da raya ayyuka a cikin jam'iyya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China