Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya bayar da amsa ga wasika da wakilan kungiyar jami'o'in kasa da kasa masu nazarin sauyin yanayi suka aike masa
2020-01-07 13:58:40        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayar da amsa ga wasikar da wakilan kungiyar jami'o'in kasa da kasa masu nazarin sauyin yanayi suka aike masa, inda ya jinjinawa matsayin da dalibai suka dauka, na mayar da hankali kan batutuwan dake shafar makomar Bil Adama, inda ya ce yana sa ran daliban za su taka rawar gani wajen kiyaye muhallin hallitun duniya.

A Ranar 17 zuwa 19 ga watan Nuwamban bara ne aka yi taron dandalin dalibai masu neman digiri na biyu na kungiyar jami'o'in kasa da kasa masu nazarin sauyin yanayi a jami'ar Tsinghua, inda daliban kungiyar suka aikawa shugaban wata wasika, don bayyana abubuwan da suka karu wajen halartar ayyukan kungiyar, da kuma tunanin da suka yi na yadda za su sauke nauyin dake wuyansu don tinkarar sauyin yanayi da ingiza sha'anin kiyaye muhalli. (Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China