Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Kiribati ta yi abin da ya dace wajen sake dawo da huldar diflomasiya da kasar Sin
2020-01-06 20:35:54        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Litinin cewa, Shugaban Kiribati Taneti Mamau da kasarsa, sun sanar da dawo da huldar diflomasiya da kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, yayin da yake ganawa da Mamau a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Tun a watan Satumban shekarar 2019 ne dai, kasashen Sin da Kiribati suka sake dawo da huldar diflomasiya a tsakaninsu, bisa manufar kasar Sin daya tak a duniya, lamarin da ya bude wani sabon babi a alakar kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China