Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da kai hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya a Mali
2019-05-20 09:48:49        cri
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan jami'an shirin wanzar da zaman lafiyar MDD a Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

Kwamitin ya fada cikin wata sanarwa cewa, mambobin kwamitin, sun yi Allah wadai da babbar murya kan harin wanda aka kaddamar da shi a ranar Asabar kan motocin jami'an shirin wanzar da zaman lafiyar MDD a Mali (MINUSMA) a yankunan Timbuktu da Tessalit.

An hallaka wani jami'in wanzar da zaman lafiya na Najeriya da kuma jikkata wani yayin da maharan suka kaddamar da harin a Timbuktu, dake arewacin Mali. Haka lamarin ya kasance a yankin Tessalit inda aka raunata wasu jami'an shirin wanzar da zaman lafiyar 3 'yan kasar Chadi.

Sanarwar ta ce, "Mambobin kwamitin sulhun MDD sun bayyana damuwarsu game da yanayin tsaro da ake ciki a Mali da kuma barazanar tsaro na hare haren ta'addanci da ake fuskanta a yankin Sahel. Sun bukaci dukkan bangarorin Mali da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar Mali ba tare da bata lokaci ba." (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China