Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mali na cikin muhimmin lokacin tabbatar da zaman lafiya
2019-06-13 13:28:54        cri
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan batun kasar Mali ya bayyana a jiya Laraba cewa, yayin da take ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankali, kasar Mali dake yammacin Afirka na cikin wani muhimmin mataki na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wakilin musamman na babban sakataren MDD kan batun kasar Mali, Mahamat Saleh Annadif ya ce, yana da yakinin cewa yarjejeniyar sulhu da aka daddale tsakanin dakaru masu dauke da makamai da gwamnatin Mali a shekara ta 2015 zai ci gaba da samar da damammaki ga yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar nan da rabi ko shekara daya.

Tun farkon shekara ta 2012 har zuwa yanzu, gwamnatin Mali tana ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya, amma ta sha fuskantar kalubaloli da dama, ciki har da juyin mulki, da sabon fadan da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen Tuareg.

Annadif ya kara da cewa, rantsar da firaministan kasar Mali Boubou Cisse a ranar 22 ga watan Afrilun bana, da rattaba hannu kan yarjejeniyar mulkin kasa da aka yi tsakanin jam'iyya mai rinjaye da jam'iyyu masu adawa da ita duk sun nuna cewa Mali ta shiga wani sabon mataki na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China