![]() |
|
2020-01-06 19:51:48 cri |
Dangane da karuwar sabanin dake tsakanin kasar Amurka da kasar Iran, Geng Shuang ya bayyana a yayin taron manema labarai a yau cewa, tsarin nuna karfin siyasa tsohon yayi ne kuma ba zai yi nasara ba. Matakin soja na rashin hankali na baya-bayan nan da kasar Amurka ta dauka, ya keta babbar ka'idar dangantakar kasa da kasa, lamarin da ya haifar da zaman tankiya a yankin. A ko da yaushe, kasar Sin tana adawa da amfani da matakan soja cikin harkokin kasa da kasa, domin ba za a iya warware matsala ta hanyar matakan soja na matsin lamba ba.
Yau Litinin, gwamnatin kasar Iran ta sanar da shiga mataki na 5 wajen dakatar da wasu tanade-tanade dake cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran. Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya yi kira ga dukkan bangarorin dake cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da su kai zuciya nesa, da kuma tsayawa tsayin daka wajen warware matsalar ta hanyar siyasa, da kiyaye yarjejeniyar bisa dukkan fannoni yadda ya kamata. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China