Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta yi barazanar daukar mataki na 5 na tauye biyayyarta ga yarjejeniyar nukiliya
2019-12-23 10:14:51        cri
Sakataren majalissar koli ta harkokin tsaron kasar Iran Ali Shamkhani, ya ce kasarsa na shirin daukar mataki na 5, na tauye biyayyarta ga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.

Ali Shamkhani ya ce, bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar, wasu manyan kasashen Turai 3 sun sha alwashin tabbatar da kare muradun Iran ta fannin tattalin arziki, to sai dai kuma wadannan kasashe sun gaza aiwatar da matakai na hakika domin cika alkawuran nasu.

Jami'in ya kara da cewa, Amurka ce ta fara tauye yarjejeniyar ta hanyar ficewa daga cikinta, kana su ma kasashen Turai suka bi sahun ta, ta hanyar yin watsi da tanade-tanaden dake kunshe cikinta. "Don haka idan Turai ta ki martaba alkawuranta, ko shakka babu mu ma za mu dauki mataki na 5," a kalaman Mr. Shamkhani.

Rahotanni na cewa, baya ga matakin fara sarrafa makamashin nukiliya a tashar karkashin kasa ta Fordow, kasar Iran ta kuma fara girke makamashin sarrafa nukiliyar, da tace sinadarin uranium zuwa mataki mafi inganci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China