Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iran ya zargi Amurka da haddasa rikici a shiyyar
2019-10-31 11:03:16        cri
Babban jami'in gudanarwar majalisar kolin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya zargi kasar Amurka da hukumomin leken asiri na kasashen yammacin duniya da laifin ruruta wutar rikici a shiyyar, tashar talabijin ta Press TV ce ta bada rahoton.

Khamenei ya ce gwamnatin Amurka da hukumomin leken asiri na yammacin duniya, su ne ke daukar nauyin wasu kasashe masu neman mayar da hannun agogo baya a shiyyar, su ne ke da alhakin haifar da rashin zaman lafiyar dake faruwa a shiyyar.

Khamenei ya bukaci kasashen shiyyar da su sanya ido, yana mai cewa, makarkashiyar da makiya ke shiryawa burinsu shi ne su wargaza zaman lafiya da tsaron kasashen dake shiyyar.

Khamenei yayi wannan tsokaci ne a lokacin bikin yaye matasan sojoji a kwalejin horas da sojojin sama ta Khatam al-Anbia dake Tehran a ranar Laraba.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, an fuskanci zanga zanga a kasashen Iraqi da Lebanon, na neman a gudanar da sauye sauye, da inganta yanayin aikin gwamnati, da samar da damammakin guraben ayyukan dogaro da kai. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China