Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Turai 6 sun shiga tsarin biyan kudi na EU da Iran
2019-12-02 11:05:22        cri

Kasashen Faransa da Jamus da Burtaniya, sun yi maraba da shawarar da gwamnatocin kasashen Belgium da Denmark da Finland da Netherlands da Norway da Sweden suka yanke, ta shiga tsarin biya kudi na INSTEX a matsayin masu hannayen jari.

Wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kasashen uku sun bayyana cewa, matakin kasashen shida na shiga wannan tsari, zai kara karfafa tsarin na INSTEX tare da nuna kokarin da kasashen Turai ke yi na halatta yin cinikayya tsakanin Turai da Iran, tare da bayyana aniyar kasashen na ci gaba da bayyana kudurinsa game da aiki da yarjejeniyar nukiliyar kasar(JCPoA)

Sanarwar ta kara da cewa, kasashen uku, sun kuma nanata muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar. Haka kuma wajibi ne kasar Iran ta cika alkawarinta karkashin wannan yarjejeniya ba tare da bata lokaci ba.

Shi dai tsarin biyan kudi na INSTEX da kasar Iran, an bullo da shi ne da nufin saukaka yin cinikayya da Iran da kaucewa takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran. Bayan da Amurkar ta janye a watan Mayun shekarar 2018 daga yarjejeiyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015. Amurka dai ta gargadi kasashen Turai game da daukar irin wadannan matakai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China