Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude kamfanin cartoon dake karkashin mallakar CMG
2020-01-05 19:58:31        cri
Yau Lahadi, ranar 5 ga watan Janairu na shekarar 2020, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya bude reshen kamfaninsa na cartoon a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Mataimakin shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci bikin kaddamar da kamfanin, ya kuma bayyana cewa, dalilin kafa kamfanin cartoon na CMG shi ne samar da yanayi mai kyau wajen ilmantar da yara da matasan kasar Sin, da karfafa aikin tsara shirye-shiryen cartoon, da kuma tsara yarjejeniyoyin yanar gizo masu inganci, ta yadda za a raya al'adu masu kyau na kasar Sin kamar yadda ake fata, da kuma kafa wani kamfanin cartoon dake kan gaba a kasa da kasa, kana da ba da gudummawa ga yaduwar al'adun Sin a fadin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China