Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labarai mafi girma a Italiya ta zanta da shugaban CMG
2019-12-17 20:34:57        cri

Kafar yada labarai mafi girma a Italiya TGCOM24 ta zanta da shugaban babban gidan rediyo da talibijin kasar Sin CMG Shen Haixiong a kwanan baya. Yayin zantawar tasu, Shen Haixiong ya amsa tambayoyin da aka gabatar masa kan kwaskwarimar kafofin yada labarai da tattalin arzikin kasar Sin, da kuma cinikayyar Sin da Amurka da batun Hong Kong.

Game da kwaskwarimar da aka yi a fannin kafofin yada labarai, Shen Haixiong ya ce, CMG ba ma kawai wata hukumar samar da shirye-shiryen rediyo da talibijin ba, ita wata sabuwar kafa ce dake tsara da kuma yada shirye-shiryen rediyo da bidiyo na ainihi.

Yayin da ya tabo maganar tattalin arzikin kasar Sin, ya ce, an yi kiyasin cewa, karuwar GDPn kasar Sin a wannan shekara za ta kai kimanin kashi 6.1 cikin dari, kuma ana sa ran yawan kudin da za a samu daga sarrafa dukiyar kasa zai kai RMB Yuan triliyan 100, wanda ya yi daidai da kwatankwacin dala dubu 10 ga kowane dan kasar. Alkaluma dake da babbar ma'ana ga kasar Sin mai mutane biliyan 1.4.

Game da batun cinikayyar Sin da Amurka kuwa, ya ce, Sin ta dade tana nacewa ga zaman lafiya, da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da cin moriya tare. Kasashen biyu sun kuma fahimci cewa, bayan ja-in-jan da suke yi, dangantaka mai karko tsakaninsu, za ta samu bunkasuwa mai dorewa nan gaba.

Yayin da ya yi magana kan batun yankin Hong Kong, Shen Haixiong ya ce, kafofin yada labarai na kasashen yamma na ba da labarai ne yadda suke so. Alal misali, a cewar Shen Haixiong, wasu matasan yankin Hong Kong sun kaiwa 'yan sanda da fararen hula hari, amma wadannan kafofin watsa labarai sun yi biris da hakan, sai dai lokacin da 'yan sanda suka mayar da martani, sai kafofin suka ba da labarin cewa, 'yan sanda sun doki dalibai.

Ya ce al'ummar Hong Kong na tafiyar da al'amura bisa doka da shari'a, don haka 'yan sanda ba za su doki dalibai ba. A hakika dai, a cewarsa wadannan matasa sun karya doka. A yanzu kuma an kuma fara aiwatar da matakan kwantar da hankalin, kuma tun tuni gwamnatin tsakiya na nacewa ga tsarin "kasa daya tsarin mulki biyu".

Rikicin da ya dabaibaye yankin ya sa al'umomin babban yanki sun fahimci cewa, ya kamata a darajta tsarin al'umma, da halin samun bunkasuwa, a kuma yi iyakacin kokarin raya tattalin arziki. Rikici ba shi da kyau, amma duk da haka ya sanya bangarori daban-daban na kasar sun kara hada kansu, domin cimma muradunsu baki daya.

Ya kara da cewa, wasu 'yan siyasa na Amurka na yunkurin fakewa da wanann batu don illata bunkasuwar kasar Sin, musamman ma bunkasuwar babban yanki, matakin da ya yi kama da tunanin cacar baka. A cewarsa, Hong Kong mai mutane miliyan 7 na iya warware matsalarsa, karkashin taimakon gwamnatin tsakiya, kuma yana iya dogaro da babban yanki.

Ya ce Macao ya zama abun misali, inda aka kusan taya murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin na Macao hannun babban yankin, tattalin arzikin yankin da ya samu bunkasuwa mai kyau, ya ninka har sau 8. Jama'ar yankin Macao na da kwarin gwiwar samun ci gaba mai dorewa ta dogaro da babban yanki. Suna kuma ganin cewa, za su koyi darasi daga Hong Kong, don darajta zaman lafiya da karko. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China