Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hong Kong ya karbi baki mafi karanta cikin shekaru 16 sakamakon tashe tashen hankula dake aukuwa
2019-11-28 10:43:14        cri

Wasu alkaluman kididdiga da aka fitar sun nuna raguwar baki masu ziyartar yankin Hong Kong na kasar Sin, raguwar bakin da ta kasance mafi tsanani da yankin ya taba fuskanta cikin shekaru 16 da suka gabata.

Alkaluman wadanda ofishin lura da hada hadar cinikayya da raya tattalin arziki na gwamnatin yankin ya fitar, sun nuna cewa, tsakanin watannin Yuli da Satumbar bana, mutane miliyan 11 da dubu dari 9 ne kacal suka shiga yankin na Hong Kong, adadin da ya ragu da kaso 26 bisa dari cikin shekara guda, wanda hakan ya sabawa 'yar karuwar da aka samu cikin watanni 3 na farkon shekarar.

Har ila yau, adadin masu zuwa yawon bude ido yankin shi ma ya ragu da kusan kaso 40 bisa dari cikin shekara guda, zuwa watan Oktoban da ya shude, ya kuma kara raguwa da kaso 50 bisa dari ya zuwa tsakiyar watan Nuwambar nan.

Sakamakon hakan kuma, alkaluman sun nuna cewa, matsakaicin adadin masu kama dakunan otal a yankin shi ma ya yi kasa, zuwa kaso 72 bisa dari a watanni 3 na kusa da karshen shekarar ta bana, sabanin kaso 91 bisa dari da aka samu a makamancin lokaci na bara.

Hakan ya kuma haifar da karuwar rashin aikin yi, a fannonin sayayya, da sauran al'amura masu nasaba da yawon bude ido kamar karbar haya, da samar da wuraren kwana da hidimar abinci, wanda ya daga zuwa kaso 3.9 bisa dari tsakanin watanni Agusta zuwa Oktoban shekarar, adadi mafi yawa na raguwar da aka samu tun bayan farkon shekarar 2017.

Idan kuwa aka kwatanta da watanni 3 na biyun farkon shekarar, adadin wadanda aka dauka aiki a wadannan fannoni ya ragu da kusan mutum 47,000.

A matsayinsa na sashe dake sahun gaba a fannin samar da guraben ayyukan yi, a shekarar 2017 fannin yawon shakatawa na Hong Kong, ya samar da guraben aiki sama da 250,000, adadin da ya samar da kaso 4.5 bisa dari na daukacin GDPn yankin. Cikin wadannan watanni 3, GDPn yankin na Hong Kong ya ragu da kaso 2.9 bisa dari, raguwar da ta kai kaso 0.4 bisa dari kan wadda aka samu cikin watanni 3 na biyu na shekarar ta bana. Hakan ya kuma haifar da karuwar rashin ayyukan yi da kaso 3.1 bisa dari tsakanin watanni Agusta da Oktoban wannan shekara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China