Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bayyana dangantakar Sin da Masar a matsayin mai kyakkyawar makoma
2019-12-31 09:50:17        cri
Hani Azer, mamban majalisar bada shawara ga shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al- Sisi, ya ce dangantakar dake tsakanin Masar da Sin, na da karfi sosai da kuma kyakkyawar makoma.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Hani Azer ya kara da cewa, baya ga karfin dangantaka, kasashen na hadin gwiwa a muhimman fannoni da dama.

Har ila yau, jami'in ya ce kasar Sin ta zuba dimbin jari a Masar, kuma tuni ta fara aiwatar da manyan ayyuka a fannoni da dama, kamar na layukan dogo da makamashi da gine-gine da ababen more rayuwa.

A cewar wata kididdiga daga kasar Sin, ya zuwa shekarar 2018, jimilar jarin da Sin ta zuba a Masar ya zarce dala biliyan 7, wanda ya samar da ayyukan yi kai tsaye ga 'yan kasar kimanin 30,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China