Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Masar ya bayyana matsayin Sin kan batun Xinjiang
2019-12-06 13:33:58        cri

Jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang, ya zanta da manema labarai a jiya Alhamis a Alkahira dangane da matsayin Sin kan batun yankunan Hong Kong da Xinjiang. Kafofin yada labarai fiye da 10 da masana da dama sun halarci taron, ciki har da jaridar Pyramid.

Liao Liqiang ya ce, majalisar dokokin Amurka ta zartas da wata doka wai dokar hakkin Bil Adama na Uygur na shekarar 2019, wadda ta illata halin da Sin ke ciki kan hakkin Bil Adama a jihar Xinjiang, har ta shafawa kasar Sin bakin fenti game da kokarin da take yi na kawar da tsattsauran ra'ayi da yaki da ta'addanci, shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Sin na nuna matukar rashin jin dadi da kin yarda da hakan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China