Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Masar: Fasahar Sin ta fuskar yaki da cin hanci da karbar rashawa abin koyi ne
2019-12-09 14:10:57        cri

Farfesa Nadia Helmy wadda ke nazarin siyasa a jami'ar Beni Suef, ta shedawa manema labarai kwanan baya a birnin Alkahira cewa, Sin na samun ci gaba mai armashi a fannin yaki da cin hanci da karbar rashawa abin koyi ne ga Masar, tana kuma fatan bangarorin biyu za su kara hadin kai a wannan fanni karkashin tsarin dandalin tattaunawar Sin da Afrika.

A cewar Helmy, Sin ta cimma nasara mai yakini a wannan fanni, a sa'i daya kuma, ta yi hadin kai da sauran kasashe don farautar wadanda suka aikata wannan laifi a ketare, tare da dawo da dukiyoyi masu dinbin yawa.

Ban da wannan kuma, Helmy ta ce, Masar na mai da muhimmanci sosai a wannan fanni, kuma hukumar binciken harkokin mulki ta kasar Masar ta cimma nasarar gano wasu jami'an da suka aikata laifin cin hanci.

Ta kara da cewa, kamata ya yi hukumar ta yi koyi darasi daga kasar Sin a wannan fanni, tare da gayyatar wasu masana da su ba da ilmi a Alkahira a wannan fanni, don karawa ma'aikatan hukumar ilmi wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China