Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta yiwa majalisar ministocin kasar garambawul
2019-12-23 10:26:40        cri
Fadar shugaban kasar Masar ta sanar a ranar Lahadi cewa an yiwa majalisar ministocin kasar garambawul bayan samun amincewar majalisar dokokin kasar.

Daga cikin sauye-sauyen da aka yi sun hada da hadewa ma'aikatar yawon bude ido da ta al'adun gargajiya waje guda, sai kuma sake maido da ma'aikatar yada labarai bayan dakatar da ita a shekarar 2014.

Dan majalisar dokokin kasar Masar Nader Mostafa, wanda mamba ne a kwamitin yada labarai na majalisar dokokin kasar, ya yabawa matakin garambawul din a majalisar ministocin kasar, yana mai cewa, hakan ya nuna gwamnatin kasar ta fahimci muhimmancin da ma'aikatun kasar ke da shi da kuma bukatar da ake da shi na kowace ma'aikata.

Yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, dan majalisar ya ce, hade ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido waje guda zai bayar da kyakkyawar damar tafiyar da ayyukan ma'aikatun yadda ya kamata.

Haka zalika ya ce, sake dawo da ma'aikatar yada labarai yana da matukar muhimmanci, matakin zai kawo karshen yunkurin da wasu kafafen yada labarai ke yi na zubarwa kasar Masar kimarta.

Bugu da kari, kakakin majalisar dokokin kasar, Ali Abdel-Aal ya sanar da gurbin kujerar dan majlisar dokokin kasar Heikal, kasancewar shi ne sabon ministan yada labaran kasar, gabanin hakan shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin kasar Masar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China