Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Masar da Afirka ta kudu sun sha alwashin bunkasa alakar kasashen su
2019-12-11 10:12:07        cri
A jiya Talata ne shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya bayyana cewa, shi da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, sun amince da daukar matakan bunkasa hadin gwiwar kasashen su daga dukkanin fannoni.

Shugaba Sisi ya bayyana hakan ne ta wani sakon talabijin da ya gabatar yayin taron manema labarai, bayan kammala ganawa da Mr. Ramaphosa, yana mai cewa ya samu zarafin gudanar da tattaunawa mai zurfi da shugaba Ramaphosa kan batutuwa daban daban, sun kuma cimma matsayar fadada, da inganta hada hadar cinikayya, da daukar karin matakan bunkasa zuba jari tsakanin sassan biyu.

Game da halin da ake ciki a shiyyar da suke kuwa, shugaba Sisi ya ce sun tabbatar da bukatar ci gaba da tsare-tsare, wadanda za su tallafawa samar da daidaito da tsaro a nahiyar Afirka. Shugaban na Masar ya kuma jaddada wajibcin warware rashin jituwa dake wakana a wasu sassan nahiyar, da aiwatar da manufar nan ta "dakatar da jin karar bindigogi", tare da ingiza ci gaban nahiyar, da samar da karin ababen more rayuwa.

Sisi ya kuma nanata muhimmancin tabbatar da manufar nan ta "Afirka ta ceci kanta" ta hanyoyi mafiya dacewa da hakikanin yanayin da nahiyar ke ciki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China