![]() |
|
2019-12-28 16:53:42 cri |
Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin karfafa yin hadin gwiwa wajen warware rikicin kasar Libya, da kawar da mayakan 'yan tada kayar baya, da kungiyoyin ta'addanci, kana da batun kawo karshen yin shisshigin kasashen waje a harkokin cikin gidan Libyan, kakakin shugaban kasar Masar Bassam Radi ya bayyana cikin wata sanarwa.
Tattaunawar ta El-Sisi da Putin ta zo ne bayan da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bada sanarwa a ranar Alhamis cewa Turkiyya zata tura dakaru zuwa kasar Libya bisa ga bukatar da gwamnatin Libyan wacce MDD ta amince da ita ta nema nan da wata mai zuwa.
Masar ta nuna damuwa game da kan iyakar kasar mai tazarar kilomita 1,200 da Libya dake yammacin kasar inda mayaka da masu fasa kwaurin makamai ke cin karensu babu babbaka tun daga shekarar 2011.
A ranar 11 ga watan Disamba, El-Sisi ya sanar da cewa za'a kaddamar da cikakken shirin warware rikicin Libya nan da wasu watanni masu zuwa.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China