Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana dukufa wajen kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa
2019-12-30 13:34:38        cri
A karshen shekarar bana, an samu abkuwar wasu batutuwa guda biyu da suka sanya al'ummomin kasa da kasa damuwa.

Daya daga cikinsu shi ne, yadda kasar Amurka ta hana kotun sauraron kara ta WTO samun isassun alkalan da take bukata, lamarin da ya hana kotun gudanar da ayyukanta, tare da haifar da babbar illa ga tsarin cinikin da ya shafi bangarori daban daban na duniya.

Sa'an nan dayan batun da ya abku shi ne, an gaza cimma sakamako a taron sauyin yanayi na MDD da ya gudana a birnin Madrid na kasar Sifaniya.

Duk da cewa wadannan batutuwa guda biyu ba su da wata cikakkiyar alaka a tsakaninsu, amma sun nuna mana matsala guda daya, wato yanzu ana fuskantar babban kalubale wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Dole ne mu warware wannan matsala cikin sauri. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da bangarori daban daban bisa ka'idojin yin musayar ra'ayoyi, da gudanar da ayyukan tare, da more sakamako tare, inda ba kawai za ta kasance mai ba da ra'ayoyi ba, har ma za ta aiwatar da ayyukan da abin ya shafa yadda ya kamata, domin kyautata tsarin kasa da kasa cikin yanayin adalci, da kuma ba da tabbaci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ta yadda za a haifar da alfanu ga gamayyar kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China