Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya gabatar da jerin manyan labarai 10 da suka faru a kasar Sin a shekarar 2019
2019-12-30 12:52:15        cri
1. An yi bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a filin Tian'an'men a ranar 1 ga watan Oktoba na bana, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da muhimmin jawabi.

2. Cikakken zaman taro na hudu na kwamitin tsakiya karo na 19 na Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ya bude sabon zamani na "gudanar da nagartaccen mulki a kasar Sin".

3. Dukkan 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun shiga kwas mai taken "Kada a manta da buri, sa'an nan a tuna da nauyin da aka dora mana".

4. Tattalin arzikin Sin na ci gaba da bunkasuwa yadda ya kamata, an kuma cimma sakamako mai gamsarwa.

5. Manyan bukukuwa hudu da kasar Sin ta kira, ciki har da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya", wadanda suka ba da damar kafa al'umma mai makomar bai daya da ta shafi dukkanin bil Adama, tare da yunkurin samar da sabon tsarin kasa da kasa.

6. An yi bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Macao karakshin ikon kasar Sin, inda gwamnatin kasar na ci gaba da kokarin inganta manufar "kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu".

7. An fara amfani da sabon filin jiragen saman kasa da kasa na yankin Daxing na birnin Beijing, wanda ya zama daya daga cikin manyan cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama a duniya.

8. Kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta yi nasarar lashe kofin duniya na gasar na shekarar 2019, ta hanyar samun nasara a dukkan gasanni 11 da ta halarta a wannan karo.

9. Kumbon bincike na Chang'e-4 kirar kasar Sin ya turo hoton gefe mai nisa na duniyar wata, wanda ya zama irinsa na farko da aka taba dauka a wani wurin dake kusa da duniyar.

10. An fara amfani da fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin, wadda za ta inganta bunkasuwar sana'o'i daban daban cikin sauri.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China