Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana ci gaba da zuba jarin waje a kasar Sin yadda ya kamata
2019-12-30 10:03:13        cri

Ministan cinikayya na kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa, sabbin manufofi da matakan da kasarsa ta dauka, sun taimaka mata samun gagarumin ci gaba wajen tabbatar da shigar jarin waje cikin kasar a wannan shekara.

Zhong Shan ya bayyana hakan ne, yayin wani taron aiki da ma'aikatar ta shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Ya ce a cikin watanni 11 na farkon bana, ayyuka masu jarin waje wadanda aka zuba musu jarin da ya kai a kalla dala miliyan 100 sun kai 722, karuwar kaso 15.5 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Wasu alkaluma da ma'aikatar cinikayyar kasar ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu- Nuwamban wannan shekara, an kafa sabbin masa'antu masu jarin waje da yawansu ya kai 36,747, yayin da jarin waje da ya shigo cikin babban yankin kasar Sin ya kai Yuan biluyan 845.9, karuwar kaso 6 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara.

A cewar wani rahoton taron aiki game da tattalin arziki na karshen shekara da ke hasashen makomar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2020, ya nuna cewa, za a ci gaba da inganta matakan kasar na bude kofa, kana za a ci gaba da gayyato jarin waje tare da kare shi yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin za ta kara rage jerin sassa da a baya aka haramta zuba jari a ciki da ma rage harajin da ake karba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China