Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu ingantuwar iskar shaka a kasar Sin
2019-12-26 21:23:13        cri
Wasu alkaluma da ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, an samu ingantuwar iskar shaka a wasu muhimman lardunan kasar, hakan ya biyo bayan managartan matakan kula da ingancin iska da mahukuntan kasar suka dauka tun a farkon wannan shekara.

Bayanai na nuna cewa, a Beijing-Tianjin-Hebei da lardunan dake kewaya da su, a watan Nuwamba yawan kwanakin da ake samun iska mai inganci, ya tashi daga kaso 18.6 cikin 100 zuwa kaso 63 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Haka kuma, daga watan janairu-Nuwamban wannan shekara, an samu rahoton ingancin iska a sauran yankunan kasar, inda yawan sinadaran gurbata iska na PM2.5 da ke yankunan tsakiya da kudu maso yammacin kasar ya ragu da kaso 22 cikin 100 da kuma kaso 13 cikin 100 bi da bi kan makamancin lokaci na bara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China