Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara fadada dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen duniya
2019-12-29 16:37:55        cri

Tun daga ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 2019, Sin da tsibiran Solomon sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu. Kana kasar Kiribati ita ma ta mayar da dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin a watan Satumba na shekarar 2019, wacce aka yanke ta har na tsawon shekaru 16. Firaministan tsibiran Solomon Manasseh Sogavare ya sha bayyanawa sau da dama cewa, kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasarsa da kasar Sin da zabin tsayawa matsayi mai dacewa kamar yawancin kasashen duniya, shi ne muhimmin alkawarin siyasa da kasarsa ta yi. Kuma shugaban kasar Kiribati kana ministan harkokin wajen kasar Taneti Mamau ya bayyana cewa, kasarsa ta fahimci tana bukatar abokiya kamar Sin don cimma burinta na samun ci gaba.

Kafin hakan, Sin ta riga ta kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasashe 8 na tsibiran tekun Pasifik kamar su Tonga, da Fiji da sauransu, wadanda suke da yanayin hallitu mai kyau, amma suna fama da rashin samun ci gaban tattalin arziki. A shekarar 2014 da ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba ganawa da shugabannin kasashen da suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da Sin sau biyu, inda ya bayyana cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar nuna daidaito ga kasashe manya da kanana, Sin ta nuna sahihanci da ladabi ga abokai kasashen tsibirai, tare da nuna goyon baya gare su wajen bunkasa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma inganta karfinsu na samun bunkasuwa mai dorewa. Sin ta fi son samar da gudummawa gare su don sa kaimi don su raya karfinsu da kansu, tare da yin maraba da kasashen su more fasahohin samun bunkasuwa na kasar Sin.

Bayan da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasar Salvador a watan Agustan na shekarar 2018, an samu juyin juya hali kan mulkin siyasa na kasar Salvador, an jawo hankali sosai kan makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Sabon shugaban kasar Nayib Bukele ya yi imani cewa, raya dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin zai kawo damar samun ci gaba ga kasarsa da kuma amfana wa jama'arta baki daya.

Kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Salvador, muhimmin batu ne kan yin mu'amala a tsakanin kasashen biyu, wanda ya bude kofar hadin gwiwa a tsakaninsu. Sin tana son yin kokari tare da kasar Salvador wajen kara yin mu'amala, da hadin gwiwa bisa tushen nuna girmamawar juna da dena tsoma baki a harkokin cikin gidansu don inganta dangantakarsu zuwa wani sabon mataki.

Kiyaye ka'idar Sin daya tak shi ne kudurin da babban taron MDD ya tsaida a shekarar 1971, a cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, kasa da kasa sun nuna amincewa ga ka'idar, karin kasashen duniya sun zabi yin hadin gwiwa tare da kasar Sin. Ya zuwa yanzu, kasashe 180 a cikin dukkan kasashen duniya 195 sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin, wannan ya shaida cewa, ka'idar Sin daya tak ka'ida ce da kasa da kasa da jama'arsu suka amince da ita. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China