Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Da kyar kura ta kwanta a yankin Sahel
2019-12-27 13:23:53        cri

A ranar 25 ga wata, an kai hari kan sojojin tsaron kasar Burkina Faso, wadanda suke aikin sintiri a arewa maso tsakiyar kasar, inda sojoji 11 suka rasa rayukansu. Kafin wannan ranar kuma, dakarun da ba a san su wane ne ba, sun kai hari kan sojojin tsaron kasar da fararen hula a lardin Soum da ke arewacin kasar, inda a kalla sojoji 7, da fararen hula 35 suka mutu. A shekarun baya, ana fama da barkewar hare-hare a kasar ta Burkina Faso, da ma yawancin yankin Sahel na Afirka.

Siaka Coulibaly, wani masanin al'amuran kasa da kasa na Burkina Faso, ya zanta da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, inda ya ce koma-bayan tattalin arziki, shi ne babban dalilin da ya haifar da tabarbarewar tsaro a yankin Sahel. Kaza lika mummunan yanayin muhalli ya kawo cikas ga raya aikin gona da na kiwon dabbobi, sa'an nan mutanen yankin da yawa na fama da talauci. Bugu da kari ana fama da fataucin mutane da sauran laifuffuka, lamarin da ya haifar da bullar tsattsauran ra'ayi a tsakanin al'ummun yankunan. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China