Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD ya bukaci hadin gwiwa don shawo kan kalubalen tsaro a yankin Sahel
2019-08-08 11:06:26        cri

Cikin wata sanarwar shugaba, kwamitin tsaron MDD, ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar daukacin kasashen yammacin Afirka da yankin Sahel, bisa tsare-tsaren kwamitin na gudanar da ayyuka. Kaza lika sanarwar ta yi maraba da kulla kyakkyawar alaka tsakanin kwamitin na tsaro da kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Sanarwar ta kuma jaddada damuwar kwamitin, game da kalubalen tsaro dake addabar sassan yankin yammacin Afirka da yankin na Sahel, tana mai cewa matsalolin sun hada da na 'yan ta'adda, da fashin teku, da fadan makiyaya da manoma, da na masu aikata muggan laifuka tsakanin kasa da kasa, kamar fasa kwaurin bil Adama, da fataucin makamai da miyagun kwayoyi, da hakar ma'adanai da albarkatun kasa ba bisa ka'ida ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China