![]() |
|
2019-05-17 09:37:23 cri |
Ma Zhaoxu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin zaman kwamitin tsaron MDDr game da zaman lafiya da tsaron nahiyar Afirka. Ya ce tun daga farkon wannan shekara, rundunar ta fara aiwatar da matakan wanzar da tsaro, ciki hadda dakile tabarbarewar yanayin tsaro, da samar da isassun kayayyakin aiki da ake bukata a fannin.
Ma ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su marawa wannan aniya baya, kana ita ma tawagar wanzar da zaman lafiya a Mali ko MINUSMA a takaice, bisa kudurorin da aka amince da su, ta ci gaba da tallafawa wannan runduna ta kasashe 5 da dukkanin tallafin da ya kamata.
Ya ce Sin na goyon bayan MDD bisa samar da kudaden gudanarwa da kungiyar kasashen 5 ke bukata.
A shekarar 2013 ne dai aka kafa rundunar MINUSMA, da nufin taimakawa shirin wanzar da siyasa a Mali, tare da tabbatar da tsaro, da daidaito, tare da ba da kariya ga fararen hula, da kuma kare hakkokin bil Adama a kasar.
A shekarar 2017 kuma, kasashen Sahel da suka hada da Burkina Faso, da Mali, da Nijar, da Chad da Mauritania, suka kafa wata rundunar soji ta hadin gwiwa, da nufin yaki da ayyukan ta'addanci da karya dokoki, biyowa bayan ayyukan tada kayar baya daga dakarun 'yan awaren Azbinawa, matsalar da ta karade yankin arewacin Malin tun daga shekarar 2012. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China