![]() |
|
2019-11-21 14:20:58 cri |
Zhang Jun ya bayyana haka ne jiya Laraba, yayin zaman kwamitin sulhun MDD kan dakarun hadin gwiwar G5 Sahel, kasashen da suka kunshi Burkina Faso,da Chadi, da Mali,da Mauritania da Jamhuriyar Nijar.
Yayin ganawar, Zhang Jun ya bayyana cewa, yankin Sahel yana fuskantar kalulabale mai tsanani, kuma dakarun sun taimaka matuka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ya ce, ya kamata ita ma tawagar MDD dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Mali (MINUSMA) ta taimakawa hadakar dakarun na G5 Sahel.
Jakadan ya ce, ya kamata al'ummomin kasa da kasa, su goyin bayan kokarin samar da zaman lafiya da sasantawa a kasashen dake yankin Sahel,da taimakawa kasashen Afirka magance matsalolin da nahiyar ke fuskanta bisa yanayin nahiyar ta hanyar mutunta 'yancin kasashen.
An dai kafa dakarun hadakar kasashen ne a shekarar 2017 da nufin yakar 'yan ta'adda da kungiyoyin masu dauke da makamai. (Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China