![]() |
|
2019-11-20 09:32:43 cri |
Kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ruwaito ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai na cewa, yawan mutanen da suka bar muhallansu, ya karu zuwa sama da mutum 750,000. Adadin mutanen ya ninka sama da goma kan na shekarar da ta gabata.
A cewar shirin samar da abinci na duniya, kimanin mutane miliyan 2.4 ne suke bukatar taimakon abinci a tsakiyar yankin Sahel, kuma adadin na iya karuwa, duba da yadda mutane ke ci gaba da barin muhallansu.
Dujarric ya shaidawa taron manema labarai cewa, MDD da hukumomin kula da harkokin jin kai tare da tallafin hukumomin kasashe da na yankuna, suna neman dala miliyan 700 don taimakawa wadannan kasashe uku. Yana mai cewa, kaso 47 cikin 100 kawai aka samu na agajin da ake nema.
Yankin Sahel dai, yana karshen arewacin yankin Saharan Afirka ne, wani ziri mai fadin gaske da ya taso daga gabar tekun Atilantika har zuwa tekun Meditareniya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China