Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta ce karuwar rikice-rikice ta haifar da daidaitar mutane irin wanda ba a taba gani ba a yankin Sahel
2019-06-28 09:51:24        cri

MDD ta ce karuwar rikice-rikice na tilasta raba mutane da matsugunansu da kara bukatun agajin jin kai, a wani mataki da ba a taba gani ba, a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

Yayin wani taron manema labarai, kakakin Sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric, ya ce cikin shekarar da ta gabata, kusan mutane miliyan 1 ne suka tsere daga matsugunansu saboda rikici da rashin tsaro a yankin Sahel.

Ya ce, a kasashen Burkina Faso da Mali da yammacin Niger, adadin wadanda suka rasa matsugunansu ya ninka har sau biyar, idan aka kwatanta da shakera daya da ta gabata, haka zalika yankin tafkin Chadi na fuskantar karuwar sabbin hare-hare da daidaitar mutane.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya yi gargadin cewa, rashin tsaro bai taba bazuwa cikin sauri irin haka a irin wannan babban yanki tare da shafar mutane da dama ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China