Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tunisia ta musanta yin hadin gwiwa da wani bangare na Libya
2019-12-27 10:35:10        cri
Fadar shugaban kasar Tunisia, ta ce ko alama ba ta kulla wani kawance da wani bangare na kasar Libya ba. Kuma kasar ba ta da niyyar yin hakan a nan gaba.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin Tunisia ta fitar a jiya Alhamis, ta ce shugaban kasar na kare ikon mulkin kan kasarsa, da dukkanin dama ta bin ra'ayin kashin kai na sauran kasashe, wannan kuma ba batu da za a ci gaba da muhawara a kai ba.

Kaza lika sanarwar ta jaddada cewa, karairayi, da yamadidi da ake ta yadawa tun daga Laraba, na da nasaba ne da rashin fahimta, ko rashin gane hakikanin yadda al'amura suke, ko kuma mai yiwuwa wasu ne ke kokarin bata sunan gwamnatin mai ci.

Fadar gwamnatin ta kara da cewa, dukkanin wasu karairayi, da bata suna, ba za su kautar da tunanin 'yan Tunisia daga muhimman matsalolin da suke gabansu ba, musamman ma batutuwan tattalin arziki da na zamantakewarsu.

A jiya Alhamis ne dai, ministan cikin gida na gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD Fathi Bashagha, ya yi zargin cewa kasashen Turkiyya, da Tunisia da Algeria, sun kafa wani kawance, domin tallafawa gwamnatin hadaka a birnin Tripoli. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China