Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kais Saied ya lashe zaben shugaban Tunisia
2019-10-15 10:36:33        cri

Kwarya-kwaryar sakamakon da hukumar zabe ta kasar Tunisia mai zaman kanta ta gabatar jiya Litinin ya nuna cewa, Kais Saied dan takara mai zaman kansa ya ci nasara a zagaye na biyu na babban zaben shugaban kasar, bisa kuri'un da yawansu ya kai kaso 72.71 a ranar 13 ga wata.

Hukumar zaben ta yi nuni da cewa, Nabil Karoui na jam'iyyar Heart of Tunisia ya samu kuri'un da yawansu ya kai kaso 27.29. Yawan mutanen da suka kada kuri'u a zagaye na biyu ya kai kaso 55 bisa jimillar yawan mutanen kasar baki daya.

Bisa tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Tunisia, idan ba a gabatar da korafi ga hukumar zaben ba, za a sanar da sakamakon karshe na babban zaben shugaban kasar nan da kwanaki 3 masu zuwa.

Kais Saied mai shekaru 61 a duniya ya dauki tsawon shekaru yana koyar da ilmin doka da yin nazari a jami'a. Kafin ya shiga babban zaben, bai taba yin aiki cikin gwamnatin kasar ba.

An shirya gudanar da babban zabe a Tunisia a watan Nuwanban bana. Amma sakamakon rasuwar shugaba Beji Caid-Essebsi a ranar 25 ga watan Yuli, sai aka gudanar da babban zaben kafin lokacin da aka tsara. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China