Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ayyana makokin kwanaki 7 na mutuwar shugaban kasar Tunisia
2019-07-26 11:05:57        cri

Biyo bayan mutuwar Shugaban kasar Tunisia, Beji Caid Essebsi a jiya Alhamis, Firaministan kasar Youssef Chahed, ya ayyana zaman makoki na kwanaki 7 tare da kuma yin kasa da tutocin kasar dake dukkan gine-ginen gwamnati.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce gwamnatin kasar ta kuma yanke shawarar soke duk wasu wasannin fasaha da na al'adu a fadin kasar.

Beji Caid Essebsi mai shekaru 92, ya rasu ne jiya a wani asibitin soji dake birnin Tunis.

Haka zalika a Algeria, shugaban kasar na riko Abdelkader Bensalah, ya sanar da ayyana makokin kwanaki 3 na mutuwar shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi.

Da farko a jiyan, Shugaba Bensalah ya mika ta'aziyyar kasarsa ga Firaministan Tunisia Youssef Chahed. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China