Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Tunisia Ben Ali, ya rasu a Saudiyya
2019-09-20 09:56:44        cri
Tsohon shugaban Tunisia da aka hambarar, Zine El Abidine Ben Ali, ya rasu jiya Alhamis yana da shekaru 83, a wani asibiti dake Saudiyya.

Ben Ali ya yi fama da rashin lafiya cikin makonnin da suka gabata, lamarin da ya kai shi ga kwanciya a asibitin birnin Jeddah.

Tsohon shugaban kasar ya mulki Tunisia tsawon shekaru 23, kafin ya tsere zuwa Saudiyya a farkon shekarar 2011, bayan barkewar wata gagarumar zanga-zangar da ta hambarar da mulkinsa.

Daga bisani wata kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 35 saboda samunsa da laifin almundahana da halasta kudin haram. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China