Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton wani nazari ya bayyana Kais Saied a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban Tunisia
2019-10-14 12:43:34        cri

Rahoton kamfanin nazari da bincike na Sigma Conseil na kasar Tunisia, ya bayyana dan takarar kujerar shugabancin kasar, Kais Saied, a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda ya samu kaso 76.9 na kuri'un da aka kada.

Gidan talabijin na Watanya 1 na kasar a ruwaito cewa, Nabil Karoui, na jam'iyyar Heart of Tunisia, ya samu kaso 23.1 na kuri'un.

Yayin wani taron manema labarai jiya da yamma, bayan kammala kaso 70 na aikin kidaya kuri'u, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, ta ce adadin mutanen da suka kada kuri'a a zaben zagaye na 2 a cikin kasar, ya kai kimanin kaso 57.8, sannan adadin wadanda suka kada a kasashen waje, ya kai kaso 23.5.

Shugaban hukumar Nabil Baffoun, ya ce za a rufe wasu rumfunan zabe dake kasashen waje da safiyar yau Litinin, la'akari da bambancin lokaci dake tsakaninsu da babban birnin Tunisia.

Ya kara da cewa, a yau din ne kuma za a sanar da sakamakon zagaye na 2 na zaben. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China