Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin Da Humphrey Ya Yi wa Kasar Sin Ba Shi Da Tushe
2019-12-25 14:37:55        cri

A kwanakin baya, tsohon dan jarida na kasar Birtaniya Peter Humphrey, wanda aka taba daure shi a gidan kurkuku na kasar Sin, ya bayar da labari a jaridar The Sunday Times cewa, wata yarinya 'yar birnin London mai shekaru 6 da haihuwa, ta gano wasu kalmomin Turancin da aka rubuta a kan katin Christmas da ta saya, a kantin Tesco na Birtaniya, wadanda suke dauke da sakon cewa, "Mu mutanen kasa da kasa da aka daure mu a gidan kurkuku na Qingpu dake birnin Shanghai na kasar Sin, an tilasta mana da yin ayyukan kwadago. A taimake mu ta hanyar sanar da batunmu ga hukumar kare hakkin dan Adam." Kafofin watsa labaru na kasashe yammacin duniya da dama kamar su BBC, da Sky News sun bayar da labarai, da zargi kasar Sin game da batun.

Bisa hirar musamman da kafar CGTN dake karkashin jagorancin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ta yi da kamfanin samar da kayayyakin Sin ga kantin Tesco, an ce wannan kamfani mai suna Yunguang na lardin Zhejiang dake kasar Sin, ba shi da nasaba da gidan kurkuku na Qingpu ko kadan.

An gudanar da dukkan ayyukan samar da katunan Christmas da kamfanin ke samarwa kantin Tesco ne a cikin kamfanin, kana dukkan ma'aikatan samar da kayayyakin, Sinawa ne. Kana yayin da gidan CMG ya bukaci da yin hira da kantin Tesco na Birtaniya, kantin ya ce, babu shaidu da suka nuna cewa, kamfanin samar da kayayyakin ya saba ka'idojin yin amfani da mutanen da aka daure a gidan kurkuku.

A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani da cewa, ba a tilasawa mutane 'yan kasashen waje da aka daure su a gidan kurkukun na Qingpu, su yi ayyukan kwadago ba.

Don haka, alal hakika, zargin da Humphrey ya yiwa kasar Sin karya ce ke nan, ba shi da tushe ko kadan. Kafar watsa labaru ta kasar Sin ta yi hira da bangarorin da abin ya shafa cikin hanzari, ta kuma bayar da hakikakin bayanai kan batun, tare da musunta zargin da Humphrey, da kafofin watsa labaru na Birtaniya suka yiwa kasar Sin, hakan ya kuma shaida karfinta na watsa labaru da kwarewarta.

A hakika dai, yawancin mutane ba su yi imani da maganar Humphrey ba, domin wannan mutum ya aikata laifuffuka da dama. Bisa labarin da tashar internet ta ma'aikatar tsaron al'ummar kasar Sin ta bayar, an ce, tun daga shekarar 2003, Humphrey da matarsa sun kwace sakwanni game da rayuwar jama'ar kasar Sin ba bisa doka ba, daga baya su sayar da sakwannin don samun riba. A shekarar 2013, 'yan sandan kasar Sin sun kama Humphrey, tare da yanke masa hukunci, kuma an daure shi a gidan kurkuku na Qingpu har na tsawon watanni 9. A shekarar 2015, an saki shi daga gidan kurkukun. Bayan da ya fita, ya rika zargin kasar Sin ba tare da tushe ba, domin ya rika samun kudi daga hakan.

Don haka, masu amfani da yanar gizo na kasashen waje sun duba abun da Humphrey ya yi a wannan karo, sun kuma nuna shakka da kin amincewa da shi. Fararen hula masu amfani da yanar gizo sun iya gano hakikanin batun, amma me ya sa kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya ba su gano hakikanin batun da kansu ba? Wannan ya shaida cewa, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun nuna kin amincewa ga kasar Sin sosai, suna kuma zargi kasar Sin ba tare da yin la'akari da ka'idojin watsa labaru bisa tushe ba.

Kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna yunkurin zargi kasar Sin ba tare da tushe ba, amma mutane sun san hakikakin batun. Kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ba su bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon da suka shafi yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang na kasar Sin da kafar CGTN ta gabatar a kwanakin baya ba, wannan ya shaida cewa, kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna da ma'auni biyu kan watsa labaru. Ko ka'idar watsa labaru cikin 'yanci da kasashen yammacin duniya suke bi ita ce yi wa kasar Sin zargi ba tare da tushe ba?

Ya kamata a zo kasar Sin don duba wane yanayi da ake fuskanta a kasar. Wasu mutane da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna da makarmashiyar da ba sa iya bayyanawa a fili, kuma ayyukan da suke aiwatarwa ba su da tushe, kana kasa da kasa sun san hakikakin batun, har sun nuna dariya gare su.

Don haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya kalubalanci Humphrey da cewa, idan yana son yin suna a duniya, ya kamata ya yi amfani da sabbin hanyoyi. Babu shakka mutanen da suka yi mugun aiki, da tada rikici ba za su yi tasiri a dandalin duniya ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China