Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kyautata harajin kwastam da za a buga ga wasu kayayyakin da za a shigo da su a badi
2019-12-24 13:45:58        cri

Don sa kaimi ga fadada shigar da kayayyaki, da kyautata tsarin shigar da kayayyaki, tun daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2020, kasar Sin za ta buga harajin kwastam ga kayayyaki fiye da 850, wadanda ake shigar da su zuwa kasar Sin, adadin da ya yi kasa da yawansu da aka bugawa kasashen da aka fi ba su gatanci. Kayayyakin da za a buga musu sabon harajin kwastam a wannan karo sun hada da abinci, da sabbin magunguna, da sassan na'urorin sabbin fasahohin zamani da sauransu. A ganin masana, hakan zai sa kaimi ga Sin, wajen kara bude kofa ga kasashen waje, da yin ciniki mai inganci, da kuma kara samar da zaman jin dadi ga jama'ar kasar.

Bisa kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta yi, an ce, a cikin watanni 11 na farkon bana, yawan kudin da aka samu daga kayayyakin da aka yi shige da ficen su zuwa kasashen waje a kasar Sin, ya kai Yuan triliyan 28.5. Yawan kudin da aka samu daga kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen waje ya kai Yuan triliyan 15.55, wanda ya karu da kashi 4.5 cikin dari. Kana yawan kudin da aka samu daga kayayyakin da ake shigarwa kasar ya kai Yuan triliyan 12.95, wanda ya yi daidai da na makamancin lokacin bara.

Manazarci na sashen nazarin tattalin arziki da siyasa na duniya, na cibiyar kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin Gao Lingyun, na ganin cewa, Sin na kokarin gaggauta bude kofa ga kasashen waje, don sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci. A yayin da ake gudanar da aikin, samun daidaito kan tsarin shige da fice ya fi muhimmanci.

Ya zuwa yanzu, yawan kayayyakin da aka fitar da su daga Sin zuwa kasashen waje ya kai matsayin farko a duniya. A mataki na gaba kuwa, za a maida hankali ne ga fitar da masu inganci. Gao ya bayyana cewa,

"Muna iya ganin cewa, kyautata tsarin buga harajin kwastam ga kayyayakin da ake shigar da su, ya fi muhimmanci gare mu wajen kyautata tsarin cinikin shige da fice, da tabbatar da ingancin kayayyakin da ake shigar da su, da kuma biyan bukatun bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, da zaman rayuwar jama'ar kasar a fannin kashe kudi."

Tun daga shekarar 2015, Sin ta riga ta rage harajin kwastam sau biyar kan kayyayakin zaman yau da kullum da aka shigar da su, don sa kaimi ga jama'a su rage kashe kudi a kasashen waje, da biyan bukatunsu a wannan fanni. A ganin masana, kyautata tsarin harajin kwastam a wannan karo ya maida hankali ga bukatun jama'a a fannonin zaman rayuwarsu na yau da kullum, da kuma kiyaye lafiyarsu.

Alal misali, an samu karuwar matasa wadanda suke fama da cutar suga da cutar asma a kasar Sin a shekarun baya baya nan. Don rage kudin maganin yin jinya ga wadannan cututtuka, da sa kaimi ga samar da sabbin magunguna, an kawar da dukkan harajin kwastam ga magungunan masu yin jinya ga cutar asma, da kuma kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da sabbin magungunan yin jinya ga cutar suga. Bisa sabon tsarin a wannan karo, hakan zai sa karin mutane masu fama da wadannan cututtuka biyu, su yi amfani da magunguna cikin hanzari.

Game da wannan batu, farfesa Fan Yong dake koyar da ilmin kudi da haraji a babbar jami'ar sha'anin kudi ta kasar Sin ya bayyana cewa,

"Yawan masu fama da cutar suga da cutar asma ya karu cikin sauri a kasar Sin. Wasu magunguna suna iya bada taimako wajen jinyar wadannan cututtuka, kuma rage buga harajin kwastam gare su, ya samar da gudummawa wajen tabbatar da lafiyar jama'ar kasar Sin."

Bisa sabon tsarin buga harajin kwastam, tun daga ranar 1 ga watan Janairu na badi, za a soke harajin kwastam na wucin gadi da ake bugawa dagwalon kayayyaki na Wolfram da na Niobium, da mayar da buga musu harajin kwastam na kasashe da aka fi ba su gatanci. Tun daga ranar 1 ga watan Yuli na badi, za a kara rage harajin kwastam na kasashe da aka fi ba su gatanci da aka buga wa kayayyakin fasahohin sadarwa 176. A ganin masana, hakan zai sa kaimi ga raya ciniki da kiyaye muhalli, da kuma samun ci gaba mai inganci ba tare da gurbata yanayi ba.

Ban da wannan, don raya fasahohin zamani, da nuna goyon baya ga raya sha'anin fasahohin zamani, za a rage harajin kwastam da ake buga wa sassan na'urorin sabbin fasahohin zamani. Manazarci Gao Lingyun ya bayyana cewa,  

"Yayin da ake rage harajin kwastam, za a sa kaimi ga shigar da kayayyakin fasahohin zamani cikin kasar Sin, don sa kaimi ga inganta fasahohin kasar, da samun bunkasuwa mai inganci. Idan muka kyautata tsarin shigar da kayayyaki masu inganci, za a samar da gudummawa wajen kyautata tsarin kashe kudi na kasar, da daidaita matsalolin da muke fuskanta a halin yanzu a wannan fanni." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China