Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani mai fasahar sassaka duwatsu na kasar Zimbabwe na neman sayar da karin kayayyakinsa a kasar Sin
2019-12-23 14:29:32        cri

 

Bikin bajekolin kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar Sin, wani muhimmin dandali ne da kasar Sin ta bude wa kamfanonin kasashe daban daban, domin su samu damar sayar da karin kayayyakinsu a Sin. Cikin 'yan kasuwar da suka halarci bikin da ake gudanarwa a duk shekara, har da wasu da suka zo daga nahiyar Afirka. Tendekayi Tandi, wani mai fasahar sassaka duwatsu ne dan kasar Zimbabwe, ya kuma halarci wannan biki har karo 2.

A cibiyar fasahohin al'adu ta Chitungwiza dake da tazarar kilomita 30, kudu maso yammacin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, ana jin amon bugun duwatsu, yayin da wasu masu fasahar sassaka duwatsu fiye da 10 suke gudanar da ayyukansu.

Tendekayi Tandi, mai shekaru 42 a duniya, daya ne daga cikinsu. Ya mallaki wani karamin wurin aiki a cikin wannan cibiyar fasahohin al'adu, inda yake sassaka duwatsu tare da wasu 'yan uwansa.

"Bayan da na kammala karatun jami'a a shekarar 1998, ban samu damar aiki bisa abubuwan da na koya a cikin jami'a ba, maimakon haka na mai da sassaka duwatsu, da nake da sha'awa aiki na. Wannan aikin ya gamsar da ni, ya ba ni nishadi sosai, ya sanya ina karuwa a kowace rana."

Kayayyakin duwatsu da Mista Tandi ya sassaka suna da tsare-tsare masu alaka da salon mutane, da na dabbobi. Kwarewarsa a fannin sassaka abubuwa, da salo masu kyan gani da ya kirkiro, sun sa kayayyakinsa samun karbuwa sosai a kasar Zimbabwe, har ma an ajiye wasu kayayyakinsa cikin cibiyar nuna fasahohin al'adu ta kasar. Ban da haka, ya taba sayar da kayayyakinsa a kasashen da suka hada da Jamus, da Finland, da Sweden, da Canada, da dai makamantansu.

Ko da yake abubuwan da ya saka na samun karbuwa a kasashen yammacin duniya, amma a cewar Mista Tandi, ya fi mai da hankali kan kasuwannin kasar Sin. Ya fara sha'awar kasar Sin a lokacin da aka gudanar da bikin bajekolin kayayyakin kasashe daban daban EXPO a birnin Shanghai na kasar Sin a shekarar 2010. Ya taba kwashe watanni 3 yana aiki a dakin nuna kayayyakin kasar Zimbabwe cikin farfajiyar EXPO a lokacin, inda ya kula da aikin gabatar da fasahar sassaka duwatsu ta Zimbabwe ga jama'ar Sin.

Zuwa shekarar 2018, bisa taimakon da hukumar aikin ciniki ta kasar Zimbabwe ta samar, ya halarci bikin bajekolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na farko da ya gudana a birnin Shanghai, dauke da wasu kayayyakin da ya saka. Ingancin kayayyakin, da salon musamman na Afirka da suka nuna, sun burge jama'ar kasar Sin sosai, ta yadda Mista Tandi ya samu damar sayar da manyan kayayyaki guda 34, da kananan kayayyaki fiye da 100, cikin sati guda.

Daga bisani a yayin da za a kaddamar da bikin bajekolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 a watan Nuwanban shekarar 2019, Mista Tandi ya sake yin rajistar son halartar bikin, don neman kara sayar da kayayyakinsa a kasar Sin. A cewarsa,

"A ganina kasuwannin kasar Sin su ne mafi muhimmanci a duniya. Yanzu kasashenmu 2 na zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, sa'an nan ana samun karin Sinawa da ke yawon shakatawa a Zimbabwe, gami da sayen kayayyakin duwatsun da na saka. Saboda haka ni ma na fi dora muhimmanci kan kasuwannin kasar ta Sin." 

A wajen bikin bajekolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, Mista Tandi ya sayar da manyan kayayyakin duwatsu na itace da ya saka wasu 60, jimilar da ta kafa bajinta a tarihinsa na sayar da kayayyaki.

A nasa bangare, Allan Majuru, babban darektan hukumar ciniki ta kasar Zimbabwe, ya ce baya mamaki kan yadda kayayyakin da Tandi ya sassaka ke samun karbuwa a kasar Sin. A cewarsa,

"Babbar dama da kasar Sin ke da ita a fannin sayen kayayyaki na da haske. Har yanzu kamfanonin Zimbabwe ba su shiga kasuwannin Sin sosai ba. Ina fata Zimbabwe za ta sayar da karin amfanin gona ga kasar Sin."

Shi Tendekayi Tandi ya kara da cewa, zai halarci sauran bukukuwan bajekolin da za a kira a kasar Sin, don neman sayar da karin kayayyakinsa a can. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China