Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin nune-nunen kayayyakin masana'antu bisa hadin gwiwar Sin da Afirka a kasar Kenya
2019-11-27 15:47:57        cri

Da safiyar ranar 26 ga wannan watan nan ne aka bude bikin nune-nunen kayayyakin masana'antu da aka samar, karkashin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya, inda wani jami'in kasar Kenya ya yi fatan za a kara inganta dangantakar kud da kud dake tsakanin kasarsa da kamfanonin kasar Sin ta wannan biki.

Kwamitin sa kaimi ga cinikin kasa da kasa na kasar Sin, da asusun raya Sin da Afirka, da ma'aikatar harkokin hadin gwiwar masana'antu da cinikayya, da hukumar kula da zuba jari ta kasar Kenya, su ne suka yi hadin gwiwar karbar bakuncin gudanar da bikin nune-nunen kayayyakin masana'antu karkashin hadin gwiwar Sin da Afirka na kwanaki hudu, inda kamfanonin Sin 83 daga birane da larduna 11 na Sin, da wasu wuraren kasar Kenya suka halarci bikin. Fadin wurin bikin nune-nunen ya kai muraba'in mita 4000.

Shugaban tawagar kasar Sin mai halartar bikin Wang Xiaoguang ya bayyana cewa, yayin da ake kokarin aiwatar da ayyuka 8 da aka yi kira a aiwatar a gun taron koli na Beijing, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, karuwar cinikin dake tsakanin Sin da Afirka ta kara samar da ayyukan yi, da fasahohin zamani ga nahiyar Afirka. Ya ce,"A gun bikin nune-nunen a bana, baya ga kamfanonin Sin daga birane da larduna 11 na kasar Sin, za a iya ganin kamfanoni masu amfani da jarin Sin dake kasar Kenya da dama, tare da kayayyakin da suka samar. Wannan ya shaida cewa, a kokarin shugabanni da gwamnatocin kasashen biyu a shekarun baya baya nan, an samu babban ci gaba kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya a fannonin fasahohi, da samar da kayayyaki, da samar da ayyukan yi da sauransu."

An ce, guda 7 daga cikin manyan kamfanoni mafi karfi na kasar Sin 500 sun halarci bikin a wannan karo, tare da wasu kamfanoni kanana da matsakaici, wadanda suka wakilci karfin kera kayayyaki na kasar Sin, wadanda za su shaida kayayyakinsu a fannonin ayyukan more rayuwa, da na'urori, da sadarwa, da injiyoyin aikin noma, da sarrafa amfanin gona, da motoci, da kiyaye muhalli da sauransu.

Bisa rahoton daukar nauyi da aka yiwa kamfanoni masu amfani da jarin Sin dake kasar Kenya tun daga shekarar 2018 zuwa 2019 da aka gabatar, an ce, kamfanoni masu amfani da jarin Sin dake kasar Kenya, sun samar da ayyukan yi fiye da dubu 50 a shekarar 2018, inda yawan kudin da aka zuba jari a fannin zamantakewar al'ummar kasar Kenya ya kai fiye da dala miliyan 75. Mai bada taimako ga ministan harkokin masana'antu na kasar Kenya Hyrine Nyong'a, ta nuna godiya ga masu zuba jari na kasar Sin, bisa samar da babbar gudummawa da suka yi a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma ga kasar Kenya. Tana fatan za a samu karin ci gaba kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Kenya bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da tsarin burin Kenya na shekarar 2030. Ta ce,"Muna bukatar kara yin hadin gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin. Muna bukatar jawo hankalinsu don samar da sauki ga masu zuba jari na Sin, wajen kafa kamfanonin hadin gwiwa a tsakaninsu da hukumomi masu zaman kansu na kasar Kenya. Na yi imani da cewa, bikin nune-nunen a yau, zai kara inganta dangantakar dake tsakaninsu. Akwai doguwar hanya da za a bi wajen zuba jari da samar da ayyukan yi. Muna fatan yawan GDP da kamfanonin samar da kayayyaki na kasar Kenya suka samar zai karu, daga kashi 8.5 cikin dari a yanzu zuwa kashi 15 cikin dari a shekarar 2022."

Mashawarcin jakadan Sin mai kula da harkokin tattalin arziki da cinikayya na ofishin jakadancin Sin dake kasar Kenya Guo Ce ya bayyana cewa, a halin yanzu, kamfanonin Sin fiye da dari hudu sun zo kasar Kenya, inda suka samar da ayyukan yi kimanin dubu 130 a kasar, kuma yawan ma'aikatan kasar Kenya a cikin kamfanonin Sin dake kasar ya kai kashi 90 cikin dari. Ya ce,"Yanzu ofishin jakadancin Sin dake kasar Kenya ya karfafa zukatan kamfanonin Sin wajen raya ayyukansu a kasar Kenya. Ana saran gwamnatin kasar Kenya za ta ci gaba da yin kokari wajen kyautata yanayin zuba jari, da gudanar da ayyukansu cikin sauri, don samar da sauki ga aikin zuba jari. Matakin da zai jawo karin masu zuba jari na kasar Sin, har ma da na kasashen waje zuwa kasar Kenya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, da kuma amfanawa jama'ar kasar."(Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China