Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta dauki jerin matakai don jawo jarin waje
2019-11-19 14:35:35        cri

Kwanan baya, majalisar gudanarwar kasar Sin ta kaddamar da wata takarda dangane da yadda za a kyautata yin amfani da jarin waje, inda aka ba da muhimmanci kan kula da masana'antun da 'yan kasuwa na ketare suka zuba jari a ciki, an kuma gabatar da manufofi da matakai 20 a fannonin kara azama kan zuba jari, zurfafa kwaskwarimar da ake yi kan saukaka harkokin zuba jari, kiyaye halaltattun hakkokin 'yan kasuwan waje ta fuskar zuba jari, da dai sauransu. A ranar 18 ga wata, wani babban jami'in sashen kula da harkokin jarin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, takardar ta kara ba da tabbaci kan yin adalci tsakanin masana'antu masu jarin waje da takwarorinsu na gida, lamarin da ya taimaka wajen ganin 'yan kasuwan waje sun gamsu da yadda suka saka zuba jari a masana'antun kasar Sin.

Wadannan matakai 57 da ke cikin takardar sun fi mai da hankali kan kiyaye halaltattun hakkokin 'yan kasuwan waje wadanda suka zuba jari, alal misali, kara tsara ka'idoji a fili, kara karfin kiyaye 'yancin mallakar fasaha bisa doka, kyautata tsarin ayyukan kiyaye 'yancin mallakar fasaha, goyon bayan shiga ayyukan tsara ma'auni, tabbatar da yin adalci bisa doka tsakanin 'yan kasuwa na gida da waje yayin da gwamnati ta fitar da tanda kan sayen kaya ko hidima, da dai sauransu. A fannin kara saukaka harkokin zuba jari kuwa, takardar ta nuna cewa, dole ne a rage kudin da aka kashewa wajen yin amfani da jari a wajen kasa, kara saukaka wadanda suka shirya yin aiki a kasar Sin, saukaka matakan ba da iznin kan yin amfani da filaye wajen gudanar da ayyukan jarin waje da dai makamantansu. Dangane da hakan, Zong Changqing, shugaban sashen kula da harkokin jarin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, takardar ta gabatar da bukatu filla-filla kan ayyukan jarin waje na kasar Sin, a kokarin ganin manufar ta yi aiki cikin dogon lokaci. "Matakanmu sun kara mai da hankali kan kananan fannoni. Sa'an nan kuma, an kara ba da tabbaci kan yin adalci tsakanin masana'antu masu jarin waje da takwarorinsu na gida. Haka zalika, an mai da hankali wajen ganin 'yan kasuwan waje sun gamsu da yadda jarin da suka zuba a masana'antu."

A halin yanzu yadda ake zuba jari tsakanin kasa da kasa a duniya ba shi da kyau, amma kasar Sin tana ci gaba da jawo jarin waje yadda ya kamata. Lamarin yana nasaba da jerin matakan da gwamnatin Sin ta dauka. Zong Changqing ya kara da cewa, tun a farkon wannan shekara, kasar Sin ta kaddamar da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, ta kuma fito da wasu takardu masu nasaba dangane da bai wa 'yan kasuwan waje iznin shiga kasuwar kasar Sin da karfafa musu gwiwar zuba jari. Jerin matakan da kasar Sin ta dauka domin kwantar da hankalin 'yan kasuwan waje sun karfafa gwiwarsu sosai. Alkaluma sun nuna cewa, a watanni 10 na farko na shekarar bana, yawan jarin da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 752, wanda ya karu da kaso 6.6 bisa makamancin lokaci na shekarar bara.

Ye Wei, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin jarin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya nuna cewa, nan gaba, baya ga kara bai wa 'yan kasuwan waje iznin shiga kasuwar kasar Sin, da kara azama kan yin gyare-gyare da kirkire-kirkrie a yankunan gwaje-gwaje na yin ciniki cikin 'yanci, za kuma a kara karfin jawo hankalin 'yan kasuwan waje da su zuba jari a kasar Sin da kuma kiyaye hakkokinsu. "A bangare guda, za mu inganta manufofinmu, da kyautata tsarin kasa na ba da hidima ga 'yan kasuwan waje da suka zuba jari. A wani bangaren kuma, za mu kara karfin yayata manufofinmu ta fuskar zuba jari, don fara fahimtar da 'yan kasuwan waje, za a kuma kara fahimtar matsalolin da ake fuskanta wajen aiwatar da matakan, taimaka wa masana'antu su yi amfani da matakan yadda ya kamata. Har ila yau za a karfafa gwiwar hukumomin sassan kasar da su tsara manufofi na gwaji. Za a kara karfin kiyaye halaltattun hakkokin masana'antu masu jarin waje, kyautata tsarin gabatar da kara da masana'antu masu jarin waje suka gabatar, kara azama kan kafa hukumomin karbar kararrakin masana'antu masu jarin waje, da kyautata ka'idoji da matakai don sauraron kararrakin nasu yadda ya kamata."

Zong Changqing ya ci gaba da cewa, yanzu haka yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin bai ragu ba, ana kuma kyautata tsarin zuba jarin waje. Ya kiyasta cewa, kasar Sin za ta iya cimma manufarta ta jawo jarin waje a bana. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China