2019-12-02 14:15:45 cri |
A yayin bikin na wannan karo, za a gudanar da bukukuwa da dama, kamar bikin budewa, bikin ba da lambar yabo ta zinari mai alamar kwakwa, da bikin gabatar da fina-finai, da dandalin tattaunawa batutuwan da abin ya shafa, da bikin rufewa da kuma bayar da lambar yabo da saurnasu, za kuma a gudanar da bikin fina-finai mai inganci da ya dace da bukatu da sha'awar jama'a.
Shugaban babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya bayyana a gun bikin budewar cewa, kasar Sin tana kokarin samun ci gaba a fannin fina-finai a sabon zamani da ake ciki. Rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG zai ba da gudummawa wajen sa kaimi ga kara yin mu'amala a tsakanin jama'ar kasa da kasa ta hanyar bikin fina-finai na tsibirin Hainan. Ya ce,
"Muna fatan masu tsara fina-finai daga kasashen daban-daban na duniya za su yi kokari tare don inganta dandalin bikin fina-finai na tsibirin Hainan, da samar da gudummawa ga sha'anin tsara fina-finai na duniya, tare da sa kaimi ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama."
A yayin bikin budewar, 'yan wasan kwaikwayo da masu tsara fina-finai wasu 12 sun waiwayi tarihin harkar tsara fina-finai, tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin. Inda dan wasan kwaikwayo Zhang Yi ya bayyana cewa,
"A cikin shekaru 70 da suka gabata, masu tsara fina-finai na kasar Sin sun yi kokari da samun kyakkyawan sakamako, kuma sun yi imani ga samun kyakkyawar makoma. A halin da ake ciki, yawan kudin da aka samu a fannin fina-finai a kasar Sin a bana ya zarce Yuan biliyan 60. An samu babban ci gaba a wannan sha'ani. "
An fara yin bikin fina-finai na kasa da kasa na tsibirin Hainan a shekarar 2018, wannan biki bai dade ba kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da aka ba da lambar zirare mai alamar kwakwa a bikin na wannan karo. An kasa fina-finan da za a ba su lambobin yabon kashi uku, wato fim na wasan kwaikwayo, da na gaskiya, da gajeren fim. Kuma fina-finai 1495 daga kasashe da yankuna 80 ne, suka shiga takarar neman samun lambar yabon. Za a bayyana sunayen fina-finan da suka yi nasara a yayin bikin rufewar tare da bayar da lambar yabon zinare mai alamar kwakwa a ranar 8 ga wannan wata.
An zabi mashahuriyyar 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Faransa Isabelle Huppert wadda ta sha lashe lambobin yabo ta 'yar wasan kwaikwayo mafi kwarewa a matsayin shugabar kwamitin alkalai a gun bikin. Malama Isabelle ta ce,
"A yayin bikin fina-finai na tsibirin Hainan karo na farko da aka gudanar a shekarar bara, na sadu da matasa masu tsara fina-finai na nahiyar Asiya da dama, inda muka koyi fasahohin juna. Ta hanyar fina-finai, ba fasahahin daukar fim kawai ake nunawa ba, har ma ana samar da damar haduwa da jama'a." (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China