Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hana bunkasuwar Sin ta hanyar sanya HK cikin rashin kwanciyar hankali ba shi da maana
2019-12-25 13:42:28        cri

 

Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da dokar "hakkin dan Adam da diflomasiyya na yankin Hong Kong na shekarar 2019", domin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Dangane da wannan batu, babban sakataren kungiyar hada kan al'ummomin Asiya da Afirka Nouri A.R. Hussain ya bayyana a hedkwatar kungiyar dake birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar cewa, harkokin yankin Hong Kong harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, bai kamata kasashen ketare su tsoma baki cikin harkokin yankin ba.

Ya ce, kasar Sin kasa ce mai son adalci da zaman lafiya, dukkan manufofin da take gudanarwa suna nuna halinta na hakurin juna. A fannin tattalin arziki kuma, kasar Sin tana bude kofa ga waje domin neman karin jari, da kuma karfafa hadin gwiwarta da sauran kasashen duniya. Shi ya sa, hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar sanya yankin Hong Kong cikin rashin kwanciyar hankali ba shi da ma'ana ko kadan, kasar Amurka ba za ta cimma nasara ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China